Rahotanni da ke fitowa daga arewa maso gabashin Najeriya sun nuna cewa wata da ake zargi ‘yar Boko Haram ce ta tayar da abin fashewa da ke jikinta inda ta kashe mutane akalla 12.
Harin ya kuma jikkata karin wasu mutane a lokacin da ‘yar kunar bakin waken ta tarwatsa abinda da ke jikinta a kusa da kasuwar kifi ta Konduga a jihar Borno.
‘Yan Boko Haram sun aikata kashe-kashe a jihar Borno
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Juma’a da dare da misalin karfe 9:15pm. Bayanai na ci gaba da fitowa a kan harin musamman hakikanin adadin mutane da suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka.
Shugaban ‘yan sa kai na Konduga Tijjani Ahmed ya ce abin ya auku ne a daidai lokacin da mutane suka fita shan iska tare da hira a kusa da kasuwar ta kifi.
Hanyoyin dakile ta’addanci a Najeriya
A baya-bayan nan dai hare-haren Boko Haram na dada karuwa a jihar Borno, abinda ya sa gwamna Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa a kwanakin baya.