Harin kunar bakin wake ya halaka akalla mutum 12 a Borno – DW – 06/21/2025


Rahotanni da ke fitowa daga arewa maso gabashin Najeriya sun nuna cewa wata da ake zargi ‘yar Boko Haram ce ta tayar da abin fashewa da ke jikinta inda ta kashe mutane akalla 12.

Harin ya kuma jikkata karin wasu mutane a lokacin da ‘yar kunar bakin waken ta tarwatsa abinda da ke jikinta a kusa da kasuwar kifi ta Konduga a jihar Borno.

‘Yan Boko Haram sun aikata kashe-kashe a jihar Borno

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Juma’a da dare da misalin karfe 9:15pm. Bayanai na ci gaba da fitowa a kan harin musamman hakikanin adadin mutane da suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka.

Shugaban ‘yan sa kai na Konduga Tijjani Ahmed ya ce abin ya auku ne a daidai lokacin da mutane suka fita shan iska tare da hira a kusa da kasuwar ta kifi.

Hanyoyin dakile ta’addanci a Najeriya

A baya-bayan nan dai hare-haren Boko Haram na dada karuwa a jihar Borno, abinda ya sa gwamna Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa a kwanakin baya.

Hot this week

Divadii Tazo Da Bala’i

Kai daga ganin Kura kasan za ta ci Akuya,...

Audiomack ne Manhajar da Yan Nigeria Sukafi Amfani Dashi Wajen Sauraron Wakoki.

Kusan yanzu da yawan masu sauraron wakoki da Podcast...

Tyla ya baci magoya baya yayin da ta tabbatar da hadin gwiwa tare da Wizkid

Mawaƙi nahammy-mawuyacin Tyla ya tabbatar da cewa ta...

Topics

spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img