Iyalan marigayi shugaban Zambiya, Edgar Lungu, sun sanar da cewa za a binne tsohon shugaban a Afirka ta Kudu, bayan rikici da gwamnatin Zambiya kan shirin yi masa jana’iza a hukumance.
A ranar Laraba ne dai iyalan Edgar Lungu suka hana dawo da gawarsa daga Afirka ta Kudu, inda ya rasu a asibiti ranar 5 ga Yuni, saboda an gano cewa shugaban kasa Hakainde Hichilema na shirin karbar gawar, abin da ya saba wa muradin marigayin.
A martanin da ya yi, Shugaban Zambiya Hakainde Hichilema ya rage lokacin jimamin kasa da aka ayyana sabowa marigayi Shugaba Lungu, wanda ya maye gurbinsa a 2021 bayan lashe zabe.
Mai magana da yawun iyalan, Makebi Zulu, ya ce jana’izar da binne marigayi Shugaba Lungu za su gudana ne a Afirka ta Kudu, bisa ga bukatar iyalan na yin bikin cikin sirri.