Mutane sun mutu a ruftawar ma’adini a Kwango – DW – 06/20/2025


Akalla mutane 16 ne suka mutu sakamakon rushewar mahakar ma’adinin kwal mafi girma a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, mahakar kuma da ke karkashin ikon kungiyar ‘yan tawaye ta M23 mai samun goyon bayan Ruwanda.

Tun bayan dawowar kungiyar tawayen a 2021, mayakanta sun kwace manyan yankuna masu arzikin ma’adanai a gabashin Kwangon, ciki har da ma’adinin Rubaya a lardin arewacin Kivu cikin watan Afrilun bara.

Wannan lamari ya kara munin rikicin shekaru sama da 30 da ya addabi gabashin kasar, inda kungiyoyin tawaye da kasashen waje ke fafatawa kan iko da arzikin ma’adanai masu daraja.

Ma’adinin Rubaya na samar da kashi 15 zuwa 30 cikin 100 na kwal a duniya, wanda ake amfani da shi wajen kera kayayyakin laturoni kamar kwamfutoci da wayoyin salula.

Rahotannin Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa kungiyar M23 na tara haraji daga harkokin ma’adinan da kuma fitar da albarkatun kwal zuwa Ruwanda, wanda hakan ke haifar da matsalar shigar ma’adinan rikici cikin kasuwannin duniya.

Hot this week

Divadii Tazo Da Bala’i

Kai daga ganin Kura kasan za ta ci Akuya,...

Audiomack ne Manhajar da Yan Nigeria Sukafi Amfani Dashi Wajen Sauraron Wakoki.

Kusan yanzu da yawan masu sauraron wakoki da Podcast...

Tyla ya baci magoya baya yayin da ta tabbatar da hadin gwiwa tare da Wizkid

Mawaƙi nahammy-mawuyacin Tyla ya tabbatar da cewa ta...

Topics

spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img