Kusan yanzu da yawan masu sauraron wakoki da Podcast na sauraro ne akan manhajojin wayar hannu ko kuma shafukan yanar gizo, wanda hakan ya sauya yadda kasuwar sauti take a fadin duniya baki daya. Duk da karanchin wutar lantarki da tsadar Data a Nigeria, yan kasar ba’a barsu a bayaba wajen sauraron wakoki akan mahajojin ba.
Manhajojin da suke jan zaren su a Nigeriya sun hada da Audiomack, da Spotify, da Tunecho sai Boomplay. Audiomack dai shine manhajar da yan Nigeria suka fi amfani dashi wajen sauraron wakoki kamar yadda alkaluman bincike na Similarweb suka bayyana, wannan bayani ya fito ne a watan Yuli na wannan shekara ta 2025, a yayin da Spotify ke mara masa baya sai Tunecho sai Boomplay.
A wasu alkaluman da binciken Sensor Tower suka bayyana a Kwatar farko ta shekarar 2024 sun nuna Audiomack din dai ke kan gaba a matsayin manhajar da Yan Nigeria suka fi amfani da ita wajen sauke wakokin a kan wayoyin su na hannu.
Amma duk da haka kimanin mutane Miliyan 75 zuwa Miliyan 95 ne da manhajar Boomplay wacce a ka kafa ta a Nigeria, wanda mafi yawan su yan Nigeriya ne.
Manhajar Spotify da tayi shura a fadin duniya kuwa bincike ya nuna Yan Nigeria na amfani da ita ne a kan shafukan yanar gizo (Web) akan computer ke nan sabanin wayar hannu in da a wata guda kimanin mutane miliyan 3.28 ke ziyartar manhajar wanda manhajojin Audiomack da Boomplay basa samun hakan.
A karshe binciken mu ya nuna mana cewa Audiomack ne na farko a Nigeria sai mai biye masa Boomplay wanda yake da masu amfani dashi a fadin Afirka baki daya, Sai Spotify wanda mutane suka fi amfani dashi akan shafukan yanar gizo (Web) a gida Nigeriya.
Wanne manhaja kuke amfani dashi wajen sauraron wakokin Hausa? Ku fada mana a comment section ko ku aiko mana DM a shafukanmu na sada zumunta @officialhmtv
Ana Tare