Divadii Tazo Da Bala’i

Kai daga ganin Kura kasan za ta ci Akuya, daga irin yadda take saka suttura, da yadda take rubutu a shafukan ta na sada zumunta, kai!! in ka kalli wasu wakokinta na baya kasan babu abinda ya shalli Dayyiba, domin kuwa bata kwana a duk lokacin da ta so bayyana abin da yake ranta.

Ga wadanda basu san Divadii ba zan so su ziyarci shafukanta na sada zumunta @divadii ko kuma su saurari wakokin da ta rera a baya, hakan ba zai sa kuyi mamakin sabuwar wakar ta da ta saki a kwanakin nan ba mai taken “Bala’i”.

Duk bahaushe ya san in akace “Bala’i” to ba abin alkhairi bane amma a Hausa irin ta ‘Yan GenZ Divadii tayi amfani da kalmar a hikimance wajen nuna irin karfin halin ta da jajircewar da take dashi wajen nuna halin ko’in kula ga yan bani na iya da sa’ido a rayuwarta.

Kidan wakar “Bala’i” ya jijjiga ni kwarai saboda na saurari wakar ne a lasifikoki a cikin Studiyon mu da ke nan Washington DC, salon Rap mai kama da na Cardi B ya kara wa wakar armashi a wurina, ta bangaren rubutu kuwa wakar tayi daidai da kidan duk da dai a ganina ashariyar  da Divadii ta kukkunduma a ciki bana jin akwai bukatar yin hakan. To amma kasan lamarin GenZ musamman masu jin jikin su da zafi kamar butar shayi.

Bari in yi shiru haka, ku garzaya wannan link din don sauraran wakar.

https://open.spotify.com/track/67BpXYs7TsNNx3CXrzn2Qq?si=1&nd=1&dlsi=e02eae6a5b4c4883

In kun gama ji ku bamu bayani anan ko a shafukan mu na sada zumunta Facebook, Instagram da Tiktok @officialhmtv

Ana Tare

Hot this week

Audiomack ne Manhajar da Yan Nigeria Sukafi Amfani Dashi Wajen Sauraron Wakoki.

Kusan yanzu da yawan masu sauraron wakoki da Podcast...

Tyla ya baci magoya baya yayin da ta tabbatar da hadin gwiwa tare da Wizkid

Mawaƙi nahammy-mawuyacin Tyla ya tabbatar da cewa ta...

Corbin on New Album ‘Crisis Kid,’ Clown on Stage Tour

“Do I have to be a tortured artist?”...

Topics

spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img